Kamfanin Man Fetur na Najeriya ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za a shawo kan matsalar karancin man fetur da layukan da ake fama daga ranar Laraba.
![](https://hausa24.com/wp-content/uploads/2024/04/images-897796150629779961628.jpg)
Olufemi Soneye, babban jami’in sadarwa na NNPC, ne ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Talata a Legas.
Soneye ya bayyana cewa a halin yanzu kamfanin ya mallaki sama da lita biliyan 1.5 na kayayyakin, wanda ya isa na akalla kwanaki 30.