Ga Dalilin Da Yasa Muhammadu Sanusi Ya Bijirewa Dokar Hana Bukin Sallah A Kano

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya ci gaba da gudanar da bikin Sallah Durbar na gargajiya duk da dokar da ‘yan sanda suka hana shi.


Tun da farko dai Sarkin ya jagoranci sallar idi da wa’azi a masallacin Juma’a na kofar Mata, wanda ya samu halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran ‘yan majalisar zartarwa.

An gudanar da sallar ne a masallacin sakamakon ruwan sama kamar da ya mamaye filin Idi. Sarkin da ke kan doki ya bi hanyar da ya saba komawa gida, inda ya tsaya ya karbi gaisuwa da jinjina daga daidaikun mutane da kungiyoyi a kan hanyar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta sanar da hana gudanar da bukukuwan Sallah Durbar bayan wani taron tsaro na hadin gwiwa da aka gudanar, saboda dalilai na tsaro.

Sai dai Gwamna Yusuf a cikin gaggawar mayar da martani ya nuna rashin gamsuwa da matakin, inda ya ce ‘yan sanda ba su tuntube shi ba, babban jami’in tsaro na jihar kafin ya bayyana hakan.

Scroll to Top