GARGADI!! Ka Nisanci Cin Kuɓewa Idan Kana Fama Da Wadannan Matsaloli Guda Biyu

Kuɓewa da muka fi sani sani da ladyfinger a turance, kayan lambu ne da yake da fa’idodi da yawa ga lafiyar mu. Duk da haka, kamar yawancin abinci, yawan amfani da shi na iya haifar da matsaloli ga lafiyar dan adam. Anan, zamu lissafo wadansu mutane huɗu da su guji cin yawan kuɓewa.



Mai Ciwon ciki

Kuɓewa na da carbohydrate da ake kira fructans, wanda zai iya zama matsala ga mutanen da ke da matsalolin hanji da ciwon ciki. Yawan cin kuɓewa na iya haifar da kumburi ciki da gudawa. Yana da kyau masu ciwon ciki su guji cin yawan kuɓewa.

Tsakuwar Koda (Kidney stones)

Duk da yake kuɓewa na da wadataccen tushen sinadirai daban-daban, yana kuma dauke da oxalates. Abin takaici, mafi yawan nau’in dutsen koda yana kunshe da calcium oxalate. Cin abinci mai yawan oxalates, Irin su kuɓewa, na iya ƙara haɗarin haɓakar duwatsun koda, musamman a cikin mutanen da ke da tarihin irin waɗannan batutuwa.

Bincike ya nuna cewa yawan cin kuɓewa na ƙara habakar cututtukan da muka ambata a sama. Yana kyau masu irin wannan matsalolin su rage cin kuɓewa.

Scroll to Top