Ku Daina Wannan zanga zangar da kukeyi kada Ku Bari Yan Adawa suyi Amfani daku domin Tarwatsa Kasarmu, Bola Tinubu ga Yan Nigeria
Shugaban Kasa Bola Tinubu yayi watsi da maganar Dawo da Tallafin Man Fetir Sannan yayi kira ga Yan Nigeria kan Cewa, “Kada Ku Bar Makiya Dimokuraɗiyya Su Yi Amfani Da Ku Wajen Kawo karshen Gwamnatina,” Tinubu Ga Masu Zanga-zanga
Shugaba Bola Tinubu ya bukaci masu zanga-zangar da kada su bari makiyan dimokradiyya su yi amfani da su wajen hargitsa Gwamnatinsa.
A jawabinsa da ya yi a fadin kasar a Yau Lahadi, Tinubu ya jaddada muhimmancin dimokuradiyyar da aka shafe shekaru 25 ana amfani da ita a Najeriya, ya kuma bayyana alfanun ta.
A ranar Asabar din da ta gabata ne, hotuna da bidiyo suka fito suna nuna masu zanga-zanga a Kano suna daga tutocin kasar Rasha yayin da suke rera wakoki cikin harshen Hausa, suna cewa, “Ba ma son Gwamnati mara kyau.” Da yawa daga cikin masu zanga-zangar, musamman matasa, sun yi kira da shugaban kasar Vladimir Putin na Rasha ya shiga tsakani.
An ba da rahoton cewa wani mai zanga-zangar ya gaya wa TheCable cewa, “Muna daga tutar Rasha ne saboda mun yi imanin Tinubu yana bin ajandar ubangidansa – Bankin Duniya, Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), da kuma Amurka.”
Bulama Bukarti, wani lauya kuma mai sharhi kan al’amuran zamantakewa, ya lura cewa Hotunan sun nuna yadda ake samun karuwar goyon bayan Rasha a Arewacin Najeriya. Kasar Rasha mai karfin Gabashin kasar a halin yanzu tana rikici da kasashen yammacin duniya, ana alakanta ta da juyin mulki a kasashen yammacin Afirka kamar Mali, Burkina Faso da Nijar.
Duk da cewa Tinubu bai yi magana ta musamman kan kasar Rasha ba a cikin jawabin nasa, Amma ya yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su bari makiyan dimokuradiyya su ci gaba da tsare-tsaren da suka sabawa tsarin mulkin kasar.