Cikakken Tarihin Ali Nuhu Muhammed 2024

Wannan ne takaitaccan tarihin Ali Nuhu Ali Nuhu Mohammed (an haife shi 15 Maris 1974) ya auri Mainuna Garba a shekara ta 2003 kuma sun haifi ‘ya’ya biyu. Jarumin dan Najeriya ne wanda ke rike da mukamin Manajan Darakta na Kamfanin Fina-Finai na Najeriya a yanzu. Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya nada shi a ranar Juma’a 12 ga watan Junairu 2024.

Tarihin Ali Nuhu

Kafin nadin sa, fitaccen dan wasan kwaikwayo ne kuma darakta a Najeriya. Yana fitowa a fina-finan Hausa da turanci, sannan kafafen yada labarai na kiransa da Sarkin Kannywood ko Sarki Ali. Kannywood itace masana’antar shirya fina-finan Hausa da ke da hedikwata a birnin Kanon Najeriya. Ali Nuhu ya fito a fina-finan Nollywood da na Kannywood sama da 500, kuma ya samu yabo da dama.

Ana kallon Ali Nuhu a matsayin daya daga cikin fitattun jaruman fina-finan Hausa a duniya, da kuma fina-finan Najeriya a fagen kallo, girmansa, da kudin shiga, kuma an bayyana shi a matsayin wanda ya fi samun nasara a fim din Hausa.

Tarihin Ali Nuhu

Tarihin Ali Nuhu

An haifi Ali Nuhu Mohammed a garin Maiduguri na jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya. Mahaifinsa Nuhu Poloma ya fito daga karamar hukumar Balanga ta jihar Gombe da mahaifiyarsa Fatima Karderam Digema daga karamar hukumar Bama ta jihar Borno. Ya girma a Kano. Ya halarci Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Dawakin Tofa Kano, sannan ya sami digiri na farko a fannin Geography a Jami’ar Jos. Ya yi hidimar kasa a Ibadan, Jihar Oyo. Daga baya ya yi kwasa-kwasan kan Fim.

Sana’a

Nuhu ya fara fitowa a fim din Abin sirri ne a shekarar 1999. Ya shahara da rawar da ya taka a fim din Sangaya, wanda ya zama daya daga cikin fina-finan Hausa da suka fi samun kudi a lokacin. Ali Nuhu ya yi hasashe a fina-finai da dama da suka hada da Azal, Jarumin Maza, kuma Stinda. Ya samu kyautar gwarzon dan wasa a matsayin mai bayar da tallafi a lokacin bikin bayar da lambar yabo ta Africa Movie Academy Awards a (2007). A shekarar 2019 Nuhu yayi bikin cika shekaru 20 a harkar fim.

Fina-Finan Ali Nuhu

• Sitanda
• Carbin Kwai
• Madubin Dubawa
• Last Flight to Abuja
• Blood and Henna
• Confusion Na Wa
• Wani Hanin
• Matan Gida
• Jinin Jikina
• Nasibi
• Ojukokoro
• Mansoor
• Banana Island Ghost
• Diamond In The Sky
• Dear Affy
• Mujadala
• Gida da waje
• Matan aure
• Toron giwa
• Ali zaki
• Adamsy
• Wasila
• Mai farin jini
• halwa
• Andamali
• Gidan kiso
• Gani gaka
• Hauwa kulu
• Zainabu abu
• Fati
Dadai sauransu

Karanta: Tarihin Ummi Rahab Jarumar Kannywood

Tarihin Ali Nuhu

KYAUTAR GIRMAMAWA

 • A shekarar 2005 ya lashe kyautar karramawa ta Jarumi dayafi kowa (Best actor).
 • A shekarar 2007 ya lashe kyautar karramawa ta wadda yafi kowa cikin sabbin jarumai masu tasowa ( best upcoming actor) daga 3rd africa
  movie academy award.
 • A shekarar 2008 ya lashe gasar jarumi dayafi kowanne (Best actor) daga The future Award.
 • Ashekarar 2011 ya lashe kyautar karramawa ta Jarumi dayafi kowa (Best actor) daga Zulu African film academy award.
 • Ashekarar 2012 ya lashe kyautar karramawa ta Jarumi dayafi kowa (Best actor Hausa) dagaNollywood awards.
 • Ashekarar 2013 ya shiga jerin wadanda suka cancanci kyautar karramawa ta “jarumi mai tallafawa jarumai” (Best supporting actor) daga 9th African movie academy awards.
 • Ashekarar 2013 ya lashe kyautar karramawa ta “Jarumi dayafi kowa” (Best actor ) daga Nigeria Entertainment Awards.
 • Ashekarar 2013 ya lashe kyautar karramawa ta Jarumi dayafi kowa (best actor Hausa) daga Best of Nollywood awards.
 • Ashekarar 2013 ya lashe kyautar karramawa ta “Fuskan kannywood” (Kannywood Face) daga city people entertainment awards.
 • Ashekarar 2014 ya lashe kyautar karramawa ta “Jarumi dayafi kowa” ( best actor) daga Kannywood awards.
 • A shekarar 2014 ya lashe kyautar karramawa ta Jarumi dayafi kowa daga city people entertainment awards.
 • Ashekarar 2014 ya lashe kyautar karramawa ta “dogaron Kannywood” daga arewa music and movie awards.
 • A shekarar 2015 ya lashe kyautar karramawa ta “jarumi da baida tsara” daga 19th African film award.
 • Ashekarar 2015 Jarumi dayafi kowa (Best actor Hausa) daga Best of Nollywood awards.
 • Ashekarar 2015 ya lashe kyautar karramawa ta “jarumi dayafi kowa daga Kannywood awards.
 • Ashekarar 2015 ya lashe kyautar karramawa ta ” Alkiblan kannywood ” daga Kannywood awards.
 • Ashekarar 2016 ya lashe kyautar karramawWa ta jarumi dayafi kowa (Best actor Hausa) daga best of Nollywood awards.
 • Ashekarar 2016 ya lashe kyautar karramawa ta Jarumi dayafi kowa daga arewa music and movie awards.
 • Ashekarar 2016 ya sake damu shiga cikin jerin wadanda suka cancanci ” Fuskar Kannywood) daga city people entertainment awards.
 • Ashekarar 2016 ya lashe kyautar karramawa ta ” Karramawar Nishadi” daga arewa creative industry awards.
 • Shekarar 2016 ya lashe kyautar karramawa ta ” kwararren Dan wasa” daga Wazobia Creative industry.
 • A shekarar 2017 jarumin yayi nasarar lashe kautar karramawa ta Gwarzon Jarumi Daga Northern Nigerian peace awards.
 • Ashekarar 2017 yasake lashe kautar karramawa ta fuskar kannywood daga city entertainment awards.
 • Yasake shiga jerin wadanda suka cancanci Kyautar karramawa ta Gwarzon Jarumi Daga city entertainment awards a shekarar 2017.
 • A 2019 city people entertainment awards takarramashi a matsayin Gwarzon Mai badaumarni.
 • A shekarar 2021 jarumin yayi nasarar lashe kautar karramawa ta Gwarzon Jarumi daga Northern Film Makers
 • A shekarar 2021 jarumin yayi nasarar lashe kautar karramawa ta Gwarzon Jarumi daga Nollywood Europe Golden Awards.

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top