Wasu Mutane Sun Mamaye Ma’ajiyar NEMA Da Ke FCT (Abuja), Sun Sawure Kayan Abinci

Wasu mazauna garin sun mamaye wani dakin ajiyar kaya na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Najeriya (NEMA) a babban birnin tarayya.

Vanguard ta tattaro cewa an kai samame gidan ajiyar ne a Karimo, yankin Phase 3 na babban birnin tarayya Abuja, a safiyar Lahadi.

Rahotanni sun ce mazauna garin sun kwashe kayan abinci da sauran kayayyaki.

A halin da ake ciki kuma, an baza jami’an ‘yan sanda a Abuja domin tarwatsa barayin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin.

Adeh, ya kara da cewa an shawo kan lamarin.

“Yanzu an shawo kan lamarin,” in ji ta.

Scroll to Top