Yan Wasan Manchester City 7 Da Zasu Iya Rasa Wasan Arsenal Sakamakon Jin Rauni

Manchester City za ta karbi bakuncin takwararta ta Arsenal a filin wasa na Etihad Stadium dake birnin Manchester a ranar Lahadi 31 ga watan Maris domin buga wasan mako na 30 na gasar Firimiya ta kasar Ingila.

Arsenal ce ke jan ragamar teburin Firimiya da maki 64 inda Liverpool da Manchester City ke matsayi na 2 da na 3 bi da bi da maki 63 kowanensu, Manchester City wadda Pep Guardiola yake jagoranta suna fatan ganin sun koma matsayi na daya akan teburin.

Amma akwai babban kalubalen doke Arsenal a gaban City sakamakon rauni da wasu daga cikin yan wasanta suka samu a lokacin da suke wakiltar kasashensu a wasannin sada zumunta da aka buga a makon da ya gabata.

Daga cikin ‘yan wasan City da suka samu rauni akwai Matheus Nunes, Manuel Akanji, John Stones, Kyle Walker, Kevin De Bruyne, Jack Grealish da mai tsaron raga Ederson da suka samu raunuka tun kafin zuwa hutu.

Scroll to Top