Hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC, ta shawarci masu ababen hawa da su guji yin gudu a lokacin damina saboda rashin ganin da kuma rashin kyawon hanya.
![](https://hausa24.com/wp-content/uploads/2024/03/frsc-on-duty-edited4736253691792255388.webp)
Kwamandan hukumar ta FRSC a jihar Enugu, Mista Adeyemi Sokunbi, ya ba da wannan shawarar ranar Asabar yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a Enugu.