Dalilin Da Kotu ta ce a kamo Ado Gwanja, sannan a dakatar da sauraren wakokinsa

Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, karkashin jagorancin MaiSharia Aisha Mahmud, ta ba da umarnin kamo fitaccen mawakin mata Ado Gwanja, sannan kotun ta kuma haramta wa mawakin yin waka da halartar bukukuwa har zuwa lokacin da ‘yan sanda za su kammala bincike a kansa.Wannan dai na zuwa ne bayan da Majalisar Malamai ta Jihar Kano, ta maka Ado Gwanja da wasu masu kara a kotu, kan amfani da kalaman da ba su dace ba a wakokinsu.

Kotu ta haramta wa Ado Gwanja ya sake waka, ko kuma a rika sauraren wakar sa har sai an kammala shari’ar a kotu.

Idan ba a manta ba a 2023, kotu ta gayyaci Ado Gwanja, Idirs mai wushirya, Murja Ibrahim Kunya, 442 da wasu bayan da wasu mazauna Kano suka maka su a kotu kan zargin bata tarbiyyar yara.

Wakar WAR wanda ya yi suna matuka a Arewacin Najeriya na cike da kalaman batsa da rashin kunya, wanda wasu ke ganin ci gaba da barin wannan waka da mawakin zai cigaba da tabarbarara da tarbiyyan ‘ya’ya.

Scroll to Top